Jami’an hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa, NDLEA, sun kama wani dan kasar Brazil da ya dawo gida kuma mahaifin ‘ya’ya biyu, Okolie Paulinus Nwabueze a filin jirgin saman kasa da kasa na Nnamdi Azikiwe NAIA dake Abuja bisa laifin shigo da hodar iblis casa’in da biyu (92), wanda ya hadiye kuma a karshe ya fitar da ita bayan kwanaki ana lura da shi a cibiyar Hukumar.
An kama matashin mai shekaru 53 da haihuwa wanda ya fito daga kauyen Mmaku, karamar hukumar Awgu ta jihar Enugu a ranar Juma’a 2 ga watan Satumba a lokacin da ya isa jirgin Qatar Airline da ke kan hanyar Brazil-Doha-Abuja.
KARANTA WANNAN LABARIN: 2023: Kwankwaso Ya Yi Wani Jawabi Kan Marawa Wani Dan Takarar Shugaban Kasa Baya
A cewar sanarwar da Kakakin Hukumar NDLEA, Femi Babafemi, ya fitar, “Nwabueze ya yi ikirarin cewa ya bar Najeriya zuwa Mozambique a shekarar 2004 kuma daga karshe ya koma Brazil a shekarar 2017, inda ya samu takardar izinin zama kafin ya yanke shawarar shigo da haramtattun abubuwa kan kudi dala $4,000”.
Kazalika, an kama wani mutum mai suna Aliyu Bello Kwasare mai shekaru 42 a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano dake MAKIA, kan yunkurin fitar da wani sabon sinadari mai suna Akuskura zuwa kasar Saudiyya.
Dan asalin karamar hukumar Kware dake Sokoto, wanda ke zaune a unguwar Goron Dutse a Kano, an kama shi ne a ranar Litinin 5 ga watan Satumba a yayin da ake fitar da fasinjoji a jirgin Ethiopian Airline zuwa Riyadh.
A filin jirgin saman kasa da kasa na Murtala Muhammed, MMIA dake Ikeja Lagos, an kama fakitin Tramadol 225mg da bai wuce Miliyan Daya da Dubu Tasa’in da Tara ba (1,099,000) ta hanyar hadin gwiwar hukumomin NDLEA da hukumar kwastam ta Najeriya.
Magungunan opioids na cike da kwalaye 50 masu nauyin kilogiram 2,058.90, an shigo da su ne daga kasar Pakistan ta hanyar Addis-Ababa a kan Jirgin saman Habasha, An ɓoye kayan a cikin wasu magunguna marasa sarrafawa.
Har ila yau, a ranar Juma’a 9 ga watan Satumba, an kama wani jami’in sufurin kaya, Aliyu Abubakar a dakin taro na NAHCO da ke filin jirgin sama, kan yunkurin fitar da wani abin tabar wiwi da aka boye a cikin kwalabe na Caro white body.
A wani labarin kuma, Hukumar NSCDC ta kama wani mutum da laifin Lalata da ɗiyar Yayan sa
Hukumar tsaro ta farin kaya ta Najeriya ta NSCDC ta kama wani mai suna Tyoughche Emmanuel bisa zarginsa da yin lalata da ‘yar wansa ‘yar shekara 14 (an sakaya sunanta ba).
Emmanuel, mai shekaru 38, wanda ya fito daga karamar hukumar Naka Gwe-West ta jihar Benue, jami’an NSCDC mata ne suka kama shi a Anagada, Abuja, da misalin karfe 5:30 na safiyar Juma’a, inda suka mika shi ga sashin kula da zirga-zirgar jama’a na hukumar, saboda cin zarafi da ya yi kan ‘yar uwarsa, wacce ke karkashin kulawarsa.