Shugaban Hukumar Shirya Jarabawar Kammala Makarantar Sakandire ta Ƙasa-NECO Farfesa Ɗantani Wushishi yace hukumar a halin yanzu tana bin jahohi 6 bashin Naira biliyan 1.8.
Wushishi ya bayyana haka a ranar Asabar a lokacin da yake jawabi ga Manema labaru a Minna, inda yace dalilin bashin shine Gwamnatocin Jahohin sun sha alwashin biyan kuɗaɗen jarabawar ga ɗaliban jahar su, amma suka kasa biyan kuɗaɗen.
Yace “Gwamnatocin Jahohin sun bayyana cewa zasu biya kuɗaɗen ɗaliban Jahohin su, amma basu yi ba.

KARANTA WANNAN LABARIN: Yemi Osinbajo Ya Isa Jihar Filato Domin Halartar Wani Taro
Jahohin sun haɗa da Zamfara, da Adamawa, da Kano, da Gombe, da Borno, da Jahar Niger, hukumar na bin su Naira biliyan 1.8 na ɗaliban su na shekarar 2019.”
Yace hukumar bata riƙe sakamakon Jahohin da basu biya kuɗaɗen ba, sabudda mutumtaka da tare, gami da fahimta, yana mai cewa hukumar tuni ta fara tattaunawa da Jahohin domin samun mafita.
Wushishi yayi kira ga Gwamnonin jahohin guda shida dasu yi abinda ya dace na biyan kuɗaɗen, domin baiwa hukumar NECO damar gudanar da aikace-aikacen ta.
Ya kuma tunatar da su cewa da kuɗaɗen da suke biya dasu ne hukumar ke gudanar da jarabawar, ƙari bisa ga sayen kayayyakin da ake gudanar da jarabawar.
Comments 1