Hukumar shirya jarabawa ta Ƙasa (NECO) ta fitar da jadawalin jawabarta na shekara ta 2020 ga dukkanin ɗalibai da ke rubuta jarabawar.
Shugaban hukumar Farfesa Godswill Obioma yayin kaddamar da jadawalin a ranar Talata ya ce hukumar za ta sa kyamarorin lura da take-taken jama’a a cibiyoyi da ma’adanar takardun jarabawar domin kawar da maguɗi.
Farfesa Obioma ya ce NECO za ta gudanar da jarabawarta na kammala sakandare (SSCE) daga ranar Litinin 5 ga Oktoba zuwa 18 ga watan Nuwamba, 2020.
https://dimokuradiyya.com.ng/jarabawar-neco-gwamnatin-neja-ta-biya-wa-dalibai-bashin-miliyan-200/
Ta kammala karamar sakandare kuma za a rubuta ta ne daga Litinin 24 ga Agusta zuwa 7 ga Satumba, 2020.
Masu kammala ƙaramar sakandare da suka samu matsala a jarabawar darussan lissafi da Turancin Ingilishi za su maimaita a ranakun 11 da 12 ga watan Nuwamba.
Su kuma ‘yan ajin ƙarshe a makarantar firamare za a yi tasu jarabawar a ranar 17 ga watan Nuwamba.
Shugaban hukumar ya shawarci masu rubuta dukkanin jarabwar NECO da su sauke jadawalin daga shafin hukumar www.neco.gov.ng