NECO tayi kira da Ɗalibai dasu Jefar da Jita-jitar ɗage Jarabawa, tace za’a fara 27 ga Yuni
Hukumar Shirya Jarabawar Kammala Sakandare ta sanar da cewa Jarabawar Kammala Sakandare ta Shekarar 2022 da ɗalibai ƴan Makaranta zai fara ranar Litinin 27 ga watan Yuni na shekarar 2020, ba kamar yadda ake yadawa cewa an ɗage Jarabawar zuwa wata rana.
Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Shugaban kula da Yaɗa Labaru da Sashen Hulda da Jama’a na Hukumar Azeez Sani ya fitar ga Manema labaru a Minna a ranar Asabar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ba Zamu Kawo Karshen Rajistar Masu Kada Kuri’a A Ranar 30 Ga Watan Yuni Ba — Farfesa Yakubu
Sani yayi kira ga masu ruwa da tsaki dasu jefar da batun ɗage Jarabawar zuwa wata rana ta daban.
“Ma’aikatun Ilmi, Shuwagabannin Makarantu da sauran masu ruwa da tsaki dasu jefar da duk wata Jita-jitar cewa an ɗage Jarabawar”, Inji sanarwar.
Shugaban Kula da bayanan yace matakan da aka ɗauka domin tabbatar da samun nasarar gudanar da Jarabawar duka an ɗauke su.
“Hukumar tace an ɗauki dukkanin matakai domin tabbatar da samun nasarar jarabawar ta shekarar 2022.”
Sanarwar ta bayyana cewar Jarabawar ta makarantu zata ƙare ranar 12 ga watan Ogusta na Shekarar 2022.
Comments 1