Magatakardar Hukumar Shirya Jarrabawar kammala sakandure ta Kasa (NECO), Farfesa Ibrahim Wushishi, ya yi alkawarin cewa za a fitar da sakamakon Jarrabawar Sakandare ta 2022 (SSCE) nan da kwanaki 45 bayan kammala jarrabawar karshe.
Wushishi ya bayyana haka ne a lokacin da yake sa ido kan yadda aikin SSCE ke gudana a wasu cibiyoyi a Legas.
Ana sa ran kammala jarrabawar da aka fara a watan Yuni a ranar 12 ga watan Agusta.
“Muna kan lamarin kuma muna ba da tabbacin cewa za a fitar da sakamakon jarabawar da ke gudana nan da kwanaki 45 bayan kammalawa,” in ji shi.
Ya kuma bayyana cewa dalibai 1.29 sun zana darussa 76 ne a jarabawar da ake yi.
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, Da yake tsokaci kan rashin tsaro a wasu sassan kasar, shugaban hukumar ya bayyana cewa an yi isassun shirye-shirye tare da jami’an tsaro don sa ido kan zirga-zirgar kayayyaki da ma’aikata.
“Har ila yau, muna da jami’an tsaro da za su jagorance mu. Dangane da harkar zirga-zirga, ba mu ci karo da wata matsala ta tsaro ba, kuma ba mu samu wani rahoto daga sassan kasar nan ba hatta a yankunan da muka zauna a gida, mun samu damar gudanar da jarrabawa ba tare da wata matsala ba.
“Kodayake, wasu ‘yan takarar sun rasa wasu takardu a bara sakamakon ‘zauna-a-gida’ amma an sake sarrafa wadancan takardun. Har yanzu ba mu da matsala sosai saboda muna da mutanenmu a kasa wadanda suka fahimci yanayin kalubalen tsaro kuma sun tsara hanyoyin shawo kan kalubalen a cikinsa duka. Don haka muna kan koshin lafiya,” in ji Wushishi.
Haramtacciyar kungiyar masu fafutukar kafa kasar Biafra (IPOB) ta ayyana zaman gida-gida a duk mako a yankin Kudu maso Gabas domin nuna adawa da tsare shugabanta, Nnamdi Kanu, wanda ke bin tafarkin ta’addanci.