By Ishaq Dabai
Rundunar ‘yan sandan jihar Neja ta cafke wani mutum mai suna Umar Muhammed mai shekaru 51 da ake zargi yana daya daga cikin masu samar da man fetur ga’ yan bindiga a jihar Neja.
An kama Muhammed tare da Adamu Atiku dan shekara 35 wanda ma’aikacin mai ne a gidan man Muhabbat dake Bosso Estate, Minna.Mutanen biyu, a cewar kwamishinan ‘yan sandan jihar Neja, Monday Kuryas, an cafke su da jarkuna 10 masu daukar lita 25 cike da man fetur da kuma babur.
Wanda ake zargi na farko, Mohammed, ya amsa cewa an kama su ne yayin da suke kokarin isar da man zuwa kauyen Gussassi dake yankin Maikunkele a karamar hukumar Bosso, inda ya bayyana cewa suna sayar da man ga masu aikin babur a kauyen Gussassi da kewayenta.
Kwamishinan duk da haka ya bayyana cewa an cafke wadanda ake zargin ne bayan sun samu bayanai kan irin ayyukan su a yankin.“Yawan man da suka kawo ya sabawa dokar zartarwa ta jihar Neja, wacce ta hana sayar da man fetur da yawa a cikin jarkoki ko wasu kwantena a gidajen mai a fadin jihar.
“Ana ci gaba da gudanar da bincike don sanin takamaiman wanda suke kai man fetur din,” in ji Kuryas; Kwamishinan ya tabbatar wa mutanen jihar cewa ‘yan sanda za su ci gaba da aiki don tabbatar da tsaro da kare lafiyar mutanen da dukiyoyin su.
Comments 1