By Ishaq Dabai
A kalla sama da mutane 300 ‘yan bindiga suka kashe tare da raba wasu mutane 3000 da muhallan su da kuma lalata kayayyaki na biliyoyin naira a yankin jihar Neja ta Gabas a cikin ‘yan watannin nan.
Sanata mai wakiltar jihar Neja ta Gabas a majalissar dokoki ta tarayya, Sanata Mohammed Sani Musa ya bayyana hakan cikin wata samarwa daya ya futar a yau Talata.
Ya kara da cewa a karshe watanni biyun nan ba’a sami kasa da mutane 3000 da aka raba da muhallan suba, wanda a yanzu haka suna san sanin IDP inda kuma mutane 300 suka rasa rayuwar su, sannan anyi a sarar kaya na biliyoyin naira da wanda aka lalata da kuma wanda makasan suka sace.
Sannan ya koka a dangane da yadda ‘yan bindiga suka matsa wajen kai hare hare babu kakkautwa a karshe watannin nan, ya kara da cewa yan bindigar sun matsa waje kawo har gitsi a kauyuka dake karamar hukumar Sharoro, inda ko a satin daya gabata sai da aka yanka wasu mazauna kauyuka mutum 20.
Musa ya kara da cewa ” suna yanka mutanen kauyuka kamar awaki wannan baki dayansa bamai yiwuwa bane, zamu tsaya tsayin daka wajen ganin masu laifin sun fuskanci hukuncin shari’a.
Kazalika yace lokaci yazo da za’a hada hannu da gwamnati wajen kawo karshen rasa rayuka da akeyi a ko wacce rana a karamar hukumar Sharoro da sauran yan kuna na Neja ta Gabas muna bukatar komai yazo karshe”.
“Mutanen mu basa iya tafiya mai tsawo dan zuwa gona aiki, basa iya zuwa kasuwa saboda aikace aikacen ‘yan bindiga”, a cewar sanata Musa.
Ya kira ga gwamnatin tarayya da takai jami’an tsaro zuwa garin Bassa, Magami da kuma Kukokki wanda aka janye a ‘yan watannin da suka wuce sannan a sanya jami’an sojoji a tsakanin kan iyakar Kaduna da jihar Neja.