Hukumar ba da agajin gaggawa ta kasa wato NEMA a ranar Asabar sun bayyana cewa sun ba da tallafi ga wadanda ambaliyar ruwa ya shafa a garin Daura a jihar Katsina.
Akalla gidaje 300 ne ambaliyar ruwan ya ruguza, a yayin da kuma ya mamaye dimbin shaguna da gidaje a ranar Talata zuwa Laraba. Mukaddashin shugaban karamar hukumar Daura, Abba Mato ya bayyana wannan ambaliyar ruwa a matsayin mafi munin da ya taba aukuwa a tarihin yankin.
Yankin da ambaliyar ruwan ya shafa ya hada da; Kusugu, Sabongari, Sarkin Yara da Mazoji a cikin Daura.
Daga cikin kayayyakin tallafin da NEMA suka raba sun hada da; shinkafa, masara, wake, gero, man gyada, gishiri da sauran su. Sannan har wala yau NEMA sun tallafa da kayayyakin gini da suka hada da siminti, kusa, silin, tabarmi, gidajen sauro, da sauran su.