A ci gaba da buga wasannin neman cancantar halartar gasar kwallon kafa ta duniya ta FIFA 2022, ‘yan wasan Turkiyya sun yi kunnen doki 3 da 3 da na Latvia da suka karbi bakunci.
A wasa na 3 na rukunin G da aka buga a filin wasanni na Ataturk da ke Istanbul, dan wasan Turkiyya Kenan Karaman ya jefa kwallo a minti na 2, Hakan Calhanoglu a minti na 33 sai Burak Yilmaz a minti na 52 da fara wasan. Latvia kuma ta jefa nata kwallayen ta kafar Savalnieks a minti na 35, Uldrikis a minti na 58 da Ikaunieks a minti na 79.
Shugaban Kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya kalli wasan a filin wasannini na Ataturk.
A yanzu Turkiyya da ta doke Holan da Norway a wasanninta na farko da na biyu, na da maki 7 kuma ita ce ta farko a rukunin G.
Shugaban Majalisar Dokokin Turkiyya Mustafa Sentop ya fitar da sanarwa ta shafin Twitter inda ya ce, saura kadan ‘yan wasanmu su samu cancantar halartar gasar kwallon kafa ta duniya ta FIFA 2022. Sun buga wasanni 3, suna da maki 7 da kwallaye 10.
Mataimakin Shugaban Kasar Turkiyya Fuat Oktay ma ya taya murna ga ‘yan wasan na Turkiyya da suka yi kunnen doki 3 da 3 da ‘yan wasan Latvia.