Hukumar kula da ɓangaren samar da wutar lantarki ta ƙasa NERC ta ƙara fayyace yadda farashin lantarki zai kasance.
Hukumar ta NERC ta ce ƙarin kuɗin wuta da aka yi a baya-bayan nan bai shafi mutanen da ke samun wuta ƙasa da awanni goma sha biyu a duk rana ba.
Kwamishina mai kula da harkokin shari’a da ba da lasisi na hukumar Mista Dafe Akpeneye ne ya fayyace hakan yayin wani taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar ta yanar-gizo.
A cewarsa, dukkannin abokin hulɗar kamfanonin rarraba wutar lantarki da basa samun wuta aƙalla awanni goma sha biyu a rana to basa cikin ƙarin farashin da aka yi.
A ranar ɗaya ga wannan wata na Satumba ne kamfanonin rarraba wutar lantarki suka sanar da sabon tsarin farashin wutar lantarki.
Comments 1