New York na iyakar kokarin ganin bayan berayen da aka kiyasta sun kai guda miliyan 18 wadanda ke zarya a birnin, LIB ta ruwaito.
An kiyasta cewa a shekarar 2014, akwai misalin beraye biyu ga duk mutum daya, wanda da aka kirga aka gane cewa sun kai miliyan 18.
KU KARANTA: Sojoji sun kuɗutar da tsohuwa ‘yar shekara 85 da wasu daga hannun ‘yan bindiga
Gwamnatin NYC tana don yin hayar Darektan kula da shige da ficen beraye kuma suna shirin biyan $170,000 (£140,000) ga duk wanda ya cancanci wannan matsayin.
Akwai bukatar masu neman wannan matsayi su kasance masu digiri da sauran matakai kamar yadda ake lissafo.
An cigaba da neman kwararru a harkar halaka beraye a NewYork saboda yadda suka addabi mazauna yankin.
A watan da ya gabata, Mayot Eric Adams yayi wani jawabi inda yace:
“Na bayyana cewa na tsani beraye. Kuma ina son ganin an halaka su. Muna kokarin ganin bayan berayenmu.”
2023: Zan Rage Rashin Aiki Da Kashi 50 A Shekara Ta Farko — Kola Abiola
Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PRP, Kola Abiola ya ce idan aka zabe shi a zaben 2023, zai rage rabin yawan marasa aikin yi a kasar nan.
DIMOKURADIYYA ta rawaito cewa Alkaluman baya-bayan nan da Hukumar kididdiga ta Kasa (NBS) ta fitar ya nuna cewa rashin aikin yi a Najeriya ya kai kashi 33.3 bisa dari a rubu’i na hudu na shekarar 2020.
Abiola, wanda ya yi magana a ranar Juma’a a yayin wani shiri kai tsaye a gidan Talabijin na Channels Politics Today, ya ce zai ba da fifiko mai dorewa da rarrabawa don bunkasa tattalin arzikin kasar.