A karon Farko, An bude Iyakokin kasar New Zealand, tun bayan da aka rufe su a watan Maris din shekarar 2020 Saboda bullar cutar Korona.
Ma’aikatan shige da ficen kasar za su fara karbar baƙi da yan makarantar da keda biza daga wasu kasashen duniya.
Firiministan K’asar Jacinda Ardern ya bayyana matakin a mastayin babban lamari, ya ƙara da cewa yana daga cikin lamurran da ke buƙatar taka tsantsan, amma akwai bukatar mafia yawan baƙi su kasence sun karbi riga-kafin cutar Korona, sai dai ba a buƙatar killace mutane.
Haká kuma an sake bude iyakokin kasar ta ruwa, dauke jirage masu shawagi a cikin ruwa, haka kuma an bar a kwale kwalen yawon buɗe ido na kasashen waje su rinka yin lodin kayyaki.
KARANTA WANNAM LABARIN: Harin Plateau: Wasu DA Ake Zargin Makiyaya Ne Sun Yi Ajalin Mutum 8, An Jikkata 2 A Jos
New Zealand dai ta bayyana shirin ta na sake bude iyakokin tun a watan Fabrairu, inda ta baiwa ‘yan ƙasar da suka karbi rigafin cutar Korona dake ƙasar Austaraliya damar komwa gida, yayin da wadanda ke zaune a wasu ƙasashe suka koma a watan Maris.
A watan Mayu ne , ƙasar ta fara karbar masu yawon buɗe ido daga ƙasashe 50 dake cikin tsarin bisa na kasar.
Shi dai Fannin yawon buɗe ido na daga cikin ɓangare da tsauraran dokokin cutar Korona na kasar New Zealand suka yima illa sosai.
A watan Maris din shekara 2021, yawan kuɗaɗen shigar da fannin na buɗe ido ya samar ya ragu daga kashi 5.5 zuwa kashi 2.9
Bayananda mahukunta suka fitar sun nuna cewa fannin buɗe ido na kasashen waje ya gamu da cikas sosai in da lamarin ya shafi Kusan kashi 91.5.
Haka kuma, yawan ma’aikatan da aka ɗauka a fannin na yawon buɗe ido ya ragu sosai inda kusan mutanen dubu 72, suka rasa ayyukansu acikin wannan lokacin na kulle annobar korona.