Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta fara Magana da kungiyar PSG domin ganin ta dauki dan wasa Neymar, wanda yake son barin kungiyar kuma suna son kammaka cinikin ne kafin a rufe kasuwar saye da sayar da ‘yan wasa ta wannan watan. Tun bayan kammala kakar wasan data gabata dai Neymar ya bayyana wa PSG cewa baya son cigaba da zaman kungiyar saboda haka yana fatan ganin ya koma tsohuwar kungiyarsa ta Barcelona wadda yabari shekaru biyu baya. Rahotanni sun ce dagantaka ta kara yin tsami tsakanin dan wasan kasar Brazil din, Neymar, da kungiyarsa, wato kungiyar kwallon kafa ta Paris Saint German, bayan da dan wasan ya ce ba zai kara buga mata wasa ba. Haka Zalika. tun bayan dawowa daga hutu, Neymar bai bugawa kungiyar wasa ba, kuma ga dukkanin alamu dan wasan yayi tsayuwar gwamen jaki kan aniyarsa ta tilastawa PSG kyale shi yiwa tsohuwar kungiyarsa ta Barcelona kome. Tuni dai Barcelona ta shirya ranar Talata domin fara tattaunawar karshe da kungiyar PSG akan dan wasan duk da cewa PSG din ta bayyana cewa bazata rage farashin da tayiwa dan wasan ba tun farko na fam miliyan 200. PSG dai ta bayyana wa Barcelona cewa bazata sayar da dan wasan ba idan har aka fara kakar wasa ta kasar Faransa kuma a sati mai kamawa ake saran za’a fara gasar inda PSG din take kokarin kare kambunta. Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ma tana zawarcin dan wasan sai dai abune mai wahala itama ta iya fitar da wadannan makudan kudaden wajen sayan Neymar, wanda PSG din ta zarga a matsayin mara tarbiyya.