Ita a nata burin kungiyar kwallon kafa ta PSG ta so suyi kakara da Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United da Dan wasanta Neymar da ita kuma ta dauki Dan wasanta Paul Pogba.
To sai dai tun a matakin farko masu ruwa da tsakiya na Kungiyar Manchester United dake kasar Ingila sun yi watsi da tayin na Kungiyar kwallon kafa ta PSG game da batun musayar.
Bayyanannun Rahotanni sun bayyana cewa United ta ki amincewa da batun musayar Neymar ne bisa dalili biyu kamar yadda mataimakin shugaban Club din Ed Woodward ya sanar, na farko kuwa shi ne United na fatan ci gaba da zama da Pogba, na biyu kuma albashin Neymar na yuro dubu dari 9 a kowanne mako zai shafi tattalin arzikin Club din na Manchester Unite.
A wani bangaren kuma suma Yan wasan suna da tasu ajandar, Dan wasan Birazil, Nerymar, yana da Burin komawa Kungiyar daya baro Barcelona dake kasar sufaniya.
Yayin da shima Paul Pogba ke da burin tsallakawa zuwa Real Madrid don ci gaba da murza Leda, to sai dai Manchester na ci gaba da bayyana burin kasancewa da Dan wasan.