Dan wasan gaba na PSG da Brazil Neymar ya sabunta Kwantiraginsa da kungiyar har zuwa kakar shekara ta 2025.
Dan wasan mai kimanin Shekara 29 ya ce kasantuwar yana zama cikin farin ciki a ko da yaushe a Ƙungiyar ya sanya rattaba hannu kan sabon kwantiragin.
An yi ta rade-radin cewa Neymar wanda ya haɗe da PSG a shekara ta 2017 kan kudin da ba taɓa sayen wani wasa ba zai yi bankwana da ita, cikin har da batun sake komawarsa Barcelona tsohuwar zuma a wurin shi.
Kuma tun bayan hadewarsa da kungiyar a yanzu haka ya zura kwallaye 85 cikin wasanni 112 da ya fafata mata.