Rahotanni daga Faransa sun bayyana cewa ‘yan wasa uku na kungiyar kwallon kafa ta PSG sun kamu da annobar cutar korona.
Wasu kafafen yaɗa labarai sun ce, PSG ta tabbatar da cewa Neymar na cikin ‘yan wasa uku da suka kamu da korona a ranar Laraba.
Tun farko hukumar shirya gasar Lig 1 ta Faransa ta ce, ‘yan wasa uku cikin tawagar PSG sun kamu da cutar ta korona.
Gwarzuwar gasar Faransa wadda ta sha kashi a wasan karshe na gasar zakarun nahiyar Turai a watan jiya, ba ta bayyana sauran ‘yan wasan da suka kamu ba.
Amma bayanai sun nuna cewa Neymar, Di Maria da Paredes sune ‘yan wasa uku na PSG da cutar ta kama.
Ya zuwa yanzu an dakatar da wasan farko na Lig 1 tsakanin Marselle da Saint Etien saboda ‘yan wasa hudu da aka samu na dauke da COVID-19.
Tuni aka fara wannan gasa ta ƙasar Faransa, sai dai PSG ba za ta buga wasanta ba sai nan da 10 ga watan Satumba domin ba ta cikakken hutu.