Yanzu haka hanya ta budewa tsohuwar ministar kudin Najeriya Ngozi Okonjo Iweala na zama mace ta farko kuma ‘yar Afirka ta farko da za ta zama shugabar Hukumar Kasuwanci ta Duniya wato WTO, sakamakon janyewar ministar kasuwancin Koriya ta Kudu Yoo Myung-hee dake fafatawa da ita.
Ma’aikatar kasuwancin Koriya ta Kudu tace bayan ganawa da Amurka wadda ke goyawa Myung-hee baya tare da wasu kasashen duniya, ta yanke hukuncin janye takarar ta, abinda ya budewa Okonjo Iweala kofar hawa kujerar ba tare da hamayya ba.
Yunkurin zabo shugaban da zai maye gurbin Roberto Azevedo wanda ya sauka daga kujerar a watan Agustan bara ya gamu da matsalolin sakamakon takun sakar da ake tsakanin Yan takarar guda biyu daga Najeriya da Koriya ta Kudu.
Jakadun manyan kasashen duniya sun bayyana goyan bayan su ga tsohuwar ministar Najeriya tun a watan Oktoba, amma shugaban Amurka na wancan lokaci Donald Trump ya sa kafa yaki amincewa da ita saboda abinda ya kira rashin kwarewa, matakin da ya haifar da tsaiko wajen zabo shugaban da zai jagoranci hukumar.
Jakadun kasashen duniya 164 ke gudanar da zaben wanda zai jagoranci wannan hukumar, amma kuma akwai manyan kasashen da suke hawa kujerar naki.
Kakakin Hukumar Kasuwancin ta duniya Keith Rockwell yace sai a ranar 1 ga watan Maris za’a sanya ranar gudanar da taron Majalisar gudanarwar hukumar.