Daga wakilin Dimukaradiyya Mukhtar Yakubu Kano.
Wani labarin da ya cika kafar sadarwa na kyautar Mota da Gwamnatin kasar Dubai ta bai wa fitacciyar Jarumar Saratu Gidado ya zama kanun jarudu a jiya Alhamis wanda hakan ya sa wakilin Dimukaradiyya ya nemi jin gaskiyar maganar daga bakin Saratu Gidado, in da ta bayyana masa cewar.
“Su masu yada labarin ba su saurari maganar da na yi a shafuka na ba ne, domin babu in da na ce wani ko Gwamnatin kasar Dubai sun ba ni kyautar Mota, kuma su je shafin nawa su Kara dubawa sosai.” Inji ta.
Ni abin da na ce a shafin mun je Dubai mun shiga kanti mun yi sayayyar kayan tsaraba kuma za mu koma gida Nigeria, amma ban ce an ba ni kyautar Mota ba, kawai dai na rike wata Leda mai hoton Mota a jikin ta, amma ban ce an ba ni kyautar Mota. ” a cewar ta.
Daga karshe ta yi kira ga ‘yan jarida, da su rinka tantance labarai Kafi su yada shi.
A wani labarin Kuma na daban.
Wani mutum da ake kyautata zaton shekarunsa sun kai ashirin, a ranar Laraba a garin Ogidi na karamar hukumar Ilorin ta yamma, ya kashe kansa.
An tsinci gawar sa da aka daure a kan rufin wani gini da ba a kammala ba, yana rataye.
Mazauna yankin sun yanke igiyar da aka daure a wuyansa don saukar da gawar mamacin.
Kafin ya kashe kansa, marigayin ya cire tufafinsa, Wanda ya rage daga shi Sai dan kamfai.
Harkawo hada wannan rahoton ba a bayyana dalilin da ya sa matashin ya aikata hakan ba, Amma wata majiya ta ce, ya yi korafin shiga cikin mawuyacin hali kafin ya aikata laifin.
Yawancin mazauna yankin Ogidi, wadanda suka zanta da Jaridar Daily Trust sun bayyana kaduwarsu kan lamarin.
A cewar wani mazaunin garin, wanda kawai ya sanya sunansa a matsayin Taiye: “Alao ya yi korafin shiga cikin mawuyacin hali na wani lokaci yanzu. Amma ba mu taɓa sanin zai kai aikata irin wannan aikin ba.
“Abin mamaki ne a gare mu lokacin da muka ga gawar sa a rataye bayan wani daga cikin al’umma ya ja hankalin mu zuwa gare shi”, in ji shi.
Ya kara da cewa marigayi Mai suna Alao har yanzu bai yi aure ba, kuma ba shi da yaro ko daya.
Comments 1