• Zakiya Ibrahim Abdullahi ta ce ita Bata neman mijin aure.
• Kuma ko da ta na neman ai basai tayi tallar kanta ba domin kuwa tuni duniya ta Santa .
• kana ta ce tana Nan kan baka ta akan hirar da ta yi da Jaridar Dimokuradiyya Wanda ta ce ” ya kamata Mu Yan fim murika auren junan mu” inji ta
Daga Mukhtar Yakubu.
Tsohuwar jaruma Zakiyya Ibrahim Abdullahi, ta yi kira ga ‘Yan jarida da su rinka gudanar da aikin su a bisa doron aikin jarida, a matsayin su na wadanda Allah ya dora musu nauyin fadakar da jama’a da wayar musu da kai, a kan abubuwan da su ke faruwa a duniya.
Jarumar ta yi wannan kiran ne, a lokacin da ta ke hira da wakilin jaridar Dimokuradiyya, a kan labarin da wata jarida mai suna Damagaram Post ta yi, in da ta ce, wai tana neman mijin aure.
KARANTA WANNAN LABARIN: Rayuwar hakar fim kamar Makaranta ce inji Jaruma Sapna
Jarumar ta Kara da cewar ” Sam babu wani lokaci da na taba yin hira da wani dan jarida na fada masa ina neman mijin aure, saboda haka ban san a ina suka samo labarin na su ba, kuma suka alakanta ni da shi.” Inji ta.
Ta Kara da cewar ” Idan ina neman mijin aure ba zuwa Soshiyal Midiya zan yi ba na rinka tallan kaina ba, kuma idan tallan kai ne ai mu a matsayin mu na ‘yan fim duniya ta gama sanin mu. Don haka labarin da suka yada ba gaskiya ba ne, don har na so na dauki mataki na shari’a a kan su, saboda bata mini sunan da suka yi.
“Labaran dai da jaridar Dimukaradiyya suka saka wannan har yanzu ina kan baka na na cewar, ya kamata mu ‘yan fim mu rinka Auren junan mu, kuma na san na fadi hakan, domin na ga abu ne mai kyau, mu rinka Auren junan mu, saboda muna da fahimtar juna a tsakanin mu. Domin shi aure ana son yin sa ne da fahimtar juna. ” A cewar jarumar.
Comments 2