Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo, a ranar Asabar, ya nisanta kansa daga rahotannin da ke cewa ya goyi bayan Kudu maso Gabas wajen samar da shugaban Najeriya a 2023.
Tun da fari an ta yada wasu rahotanni su na cewa Obasanjo ya ce Kudu maso Gabas za su kawo abubuwa da yawa idan aka bar su suka fitar da shugaban kasar.
An ruwaito Obasanjo ya bayyana hakan ne a lokacin da ya karbi bakuncin wani dan takarar shugaban kasa, Mao Ohuabunwa, a Abeokuta, dake jihar Ogun.
Sai dai, mai magana da yawun Obasanjo, Kehinde Akinyemi, ya ce tsohon shugaban kasar Bai fadi wannan maganar ba.
A cikin wata sanarwa da ya fitar, Akinyemi ya caccaki Ohuabunwa da cewa yana da hannu a wannan yama Didi.
Ya zargi dan takarar Shugaban kasan da yin amfani da kalaman da ba daidai ba a yunkurinsa na cimma burinsa.
Sanarwar ta kara da cewa: “Idan haka ne mai neman shugabancin kasar ya ke so ya tunkari burinsa; irin wannan hanya ba daidai ba ce.
“Ya zo nan ne kuma tsohon shugaban kasar ya karbe shi a matsayin bako a yayin bikin cikarsa shekaru 85 da haihuwa sai kawai ya je ya sauya zancen. Baba ba irin wannan mutumin bane kuma idan ta haka ne yake son cika burinsa ba hanya ce Mai kyau ba.”