Ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Dakta Isa Ibrahim Ali Pantami, ya yi watsi da rahotannin wata kafar yada labarai a yanar gizo ta yi ikirarin cewa ya sayi sabbin gidaje ya ajiye iyalinsa a ciki.
Pantami ya yi hakan ta bakin mai magana da yawunsa, Uwa Suleiman, da cikin daren Juma’a, 3 ga watan Yuli, 2020.
Uwa ta ce ya kamata a sani cewa kudin albashin da Malam Pantami ke samu a yanzu matsayin minista bai kai kudin da yake samu lokacin da yake karantarwa a Jami’ar Madina ba.
Hakazalika ba duniya ke gabbansa ba kawai ya dawo Najeriya ne domin taimakawa ci gaban kasa, kamar yadda ta tabbatar.
A wani bangare na martaninta, ta ce: “Dr Isa Pantami na daya daga cikin ‘yan tsiraru a Nijeriya da duniya ba ta dame su ba, kawai kishin kasa da sadukar da kai ya sanya ya amsa kiran dawowa gida. Domin fayyace gaskiya, ministan bai sayi gida ko daya ba a duniya tun lokacin da ya hau Minista.”
Ta ci gaba da cewa; “Daya daga cikin gidajen da aka wallafa wanda ministan ya ke zama ne tun Junairun 2017, sama da shekaru biyu kafin zama minista. Dayan gidan kuma haya ya karba tun daga ranar 17 ga Disamban 2019.” Ta tabbatar.
Jaridar Sahara Reporters ce ta wallafa hotunan wasu manya gidaje da ta ikirarin cewa Ministan Sadarwa, Dakta Isa Pantami, ya ajiye matansa uku a Abuja.