Dan wasan Adelaide, Josh Cavallo ya zama na farko daga cikin kwararrun masu taka leda da ya sanar cewar shi dan luwadi ne.
Cavallo ya yi wannan sanarwar ne a faifan bidiyo da wata budaddiyar wasika a kafar sada zumunta.
Wanda ke buga gasar A-League ya ce “yanzu ya samu natsuwa” da ya fito ya sanar da cewar shi dan luwadi ne, yana fatan sauran ‘yan wasan da ke luwadi za su sami karfin gwiwar yin hakan.
Dan wasan mai shekara 21 ya kara da cewar ya dade yana boye batun a zuciyarsa.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yan bindiga sun bukaci Milliyan 60 kafin sakin masu Ibada da sukayi garkuwa da su a niger
“Lokacin da nake girma na ga bukatar boye lamarin, saboda ina jin kunya – kunya saboda ba zan samu damar yin abin da nake so a rai na ba.”
A shekarar 2019 tsohon dan kwallon Newcastle United, Andy Brennan ya zama dan kasar Australia na farko namiji da ya sanar da shi dan luwadi ne a lokacin da yake taka leda. Yanzu yana wata kungiya Hume City, wadda ba ta kwararru ba ce..
Tsohon dan kwallon Aston Villa da Stuttgart da West Ham da kuma Everton, Thomas Hitzlsperger yana cikin ‘yan wasan da ya sanar yana luwadi, shekara daya bayan ya bar taka leda.
Tsohon dan wasan Leeds United, Robbie Rogers shi ma ya sanar cewar shi dan luwadi ne bayan da ya yi ritaya a 2013 daga baya ya koma taka leda a LA Galaxy ya kuma lashe MLS Cup.
Hakan ne ya sa ya zama dan wasa namiji da ya fito ya sanar dan luwadi ne a manyan wasannin kwararru a Amurka da ya lashe babban kofi a kasar.
Cavallo ya ce ya damu da cewar da zarar ya fito ya bayyana kansa zai ci karo da kalubalan da za su shafi sana’arsa ta taka leda, ya kara da cewar a matsayinsa na dan luwadi ya san akwai da dama da suka yi shiru abin su.