Gwamnan Jahar Akwa Ibom Udom Emmanuel yace yana so Allah ya tallafe shi ya zama Shugaban Ƙasa a Shekarar 2023, domin ceto Ƙasar, bawai ya zama Mataimakin Shugaban Ƙasa kamar yadda wasu suke faɗa.
Emmanuel na ɗaya daga cikin ƴan Takarar Shugaban Ƙasa a ƙarƙashin Jam’iyar PDP, kuma tuni ya fara ziyarce-ziyarce a Ƙasar domin neman Shawara.
KARANTA WANNAN LABARIN: INEC tayi Allah Wadai da kiran da ake yiwa Shugaban ta ya fito Takara
A taron wata addu’a data gudana a ɗakin taron Banquet dake gidan Gwamnatin Jahar Uyo ranar Lahadi, Ɗan Takarar ya jaddada cewa Najeriya na buƙatar Shugaba mai hangen nesa, wanda zai iya jagorantar Ƙasar ba tare da tsoro ba, yana mai ƙara dacewa yayi amanna cewar Najeriya zata fita daga ƙangin data ke ciki, da Shuwagabanni Jajirtattu wanda zasu iya magance matsalar Tattalin Arziki, Ilmi da sauran ɓangarori da suke neman a basu kulawa.
A cewar sa “ina neman Takara don In Zama Shugaban, to tunda na shiga dole in nemi tallafi daga Allah, domin in zama Shugaban Najeriya.
“Ina ganin yanzu Najeriya taje wurin da take buƙatar ɗauki Allah, idan bai bada ɗauki ba, to mu manta kawai da wata shekara ta 2023.