Tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo ya bayyana kansa a matsayin uban fusatttun matasa a Najeriya.
A zantawarsa da fitaccen mawakin nan Charly Boy, tsohon shugaban kasar ya bayyana cewa maganin matsalolin da ke addabar Najeriya na hannun matasan kasar nan.
A cikin wani faifan bidiyo da mawakin nan ya wallafa, Obasanjo ya bayyana cewa, domin Najeriya ta zama kasa ta gari, akwai bukatar matasa su canza yadda ake shugabancin kasar.
Ya ce a wani bangaren “Ni ne uban matasa fusattun matasa a Najeriya. Mu talakawa da kuma takaicin da muke ciki a halin yanzu ba daga Allah bane. Zabin shugabanninmu ne kuma idan har ana so a sauya wannan lamarin, toh sai matasa sun canza yanayin shugabancin kasar nan. Kuma Tsaftace abu ne mai sauki. Babu wanda zai iya yin hakan sai matasa.”
A wani labarin kuma na daban.
Abin Da Na Fada wa Bola Tinubu A Ziyarar Sa—- Obasanjo
Tsohon shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo ya bayyana tattaunawar da ya yi da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC mai mulki a 2023, Asiwaju Bola Tinubu a ganawar da suka yi kwanan nan.
Jaridar Dimokuradiyya ta ruwato cewa Asiwaju da wasu abokansa sun ziyarci Obasanjo a gidansa da ke Abeokuta a ranar Laraba.
Duk da cewa su biyun sun rufe wa manema labarak abin da ya faru a taron, amma ana hasashen ya na da danganta da zaben shugaban kasa a shekarar 2023.
Tsohon shugaban kasar wanda ya yi jawabi a wajen kaddamar da kwamitin tsare-tsare na mutum 300 kan nadin sabon Olowu na Owu, Oba Saka Matemilola, ya ce ya shaida wa Tinubu cewa ya kara wasu kalmomi guda biyu da tsohon Gwamnan Legas ya yi amfani da su kwanan nan a cikin kalmomin Yarbawa.
Ya ce: “Yanzu muna da kalmomi guda biyu a ƙamus na Yarbawa, ‘Emilokan’ da ‘Olule’. Waɗannan kalmomi guda biyu dake ƙamus yanzu ana amfani da su sosai”.
“Na tambayi Bola sai ya yi dariya. Na ce ko kalmomin suna da kyau ko ba su da shi, mun fara amfani da su.”
Idan dai za a iya tunawa, Tinubu ya yi ta cece-kuce kafin zaben fidda gwani na jam’iyyar APC ya yi amfani da wadannan kalamai inda ya bayyana cewa babu yadda za a yi shugaba Muhammadu Buhari ya samu nasarar lashe zaben shugaban kasa a 2015 ba tare da goyon bayan sa ba.