Babban Limamin cocin ‘Latter Rain Assembly’ da ke Legas Fasto Tunde Bakare, ya bada tabbacin cewa shi zai gaji shugaban kasa Muhammadu Buhari a shekara ta 2023.
Kamar yadda rahotanni su ka bayyana, Faston ya ce da zarar shugaba Buhari ya kammala wa’adin mulkinsa shi zai gaje shi.
Babban Faston ya ci gaba da cewa, wadanda ba su da labari su sani cewa, shugaba Buhari ne shugaban kasa na 15 a Nijeriya, yayin da shi kuma zai kasance na 16.
Bakare ya sa hannunsa ya dafa a kirji yana cewa: “Ina so ku san wannan a safiyar nan cewa babu abin da zai iya canza wannan kadara da sunan Ubangiji.
Idan dai ba a manta ba, shugaba Buhari ya taba tsayawa takara tare da Tunde Bakare a matsayin mataimakinsa a zaben shekara ta 2011 karkashin tsohuwar jam’iyyar CPC.