Nick Minaj

Nick Minaj Ta Yi Ritaya A Fagen Waka

Shahararriyar mawakiyar zamani ‘yar kasar Amurka, wato Nicki Minaj ta bayyana cewa; ta yi ritaya daga wake domin ta ci gaba da kula iyalanta. Mawakiyar ta bayyana hakan ne a shafinta na Twitter a ranar Alhamis.

Ta kara da cewa; ta zabi ta yi ritaya ne domin ta samu iyalan da za ta rika kula da su. Ta ce ta san masoyanta za su farin cikin jin hakan. Ta ce; ga masoyansa, su ci gaba da goya mata baya har mutuwa. “Ina sonku har karshen rayuwata.” In ji ta.

Mawakiyar tana dai soyayya da wani mai suna Kenneth Petty, kuma bayanai sun nuna cewa sun shirya kulla aure a tsakaninsu.

Baya ga wake da take yi, ta fito a wadansu fina-finan Holywood, kuma tana gabatar da wani shirin gidan Rediyo.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *