A Lokacin da yake aike wa da sakon ta’aziyyarsa ga masarautar Chikun Sanata Uba Sani Mai wakiltar Kaduna ta Tsakiya a majalisar dattijan Nageriya, ya nuna damuwar shi da girgizar zuciya, a lokacin da ya samu labarin mutuwar Sarkin.
Sanatan ya na cewa, Labarin rasuwar wannan basaraken gargajiya, kuma mai son kawo zaman lafiya ya yi matukar girgizani, fitaccen masanin, Esu Chikun mai martaba Dakta Danjuma S. Barde, MFR. Inda ya ce “Jihar Kaduna da Najeriya sun yi asarar Mai rikon al’adun gargajiya, Mai Gina tushe kuma uban Al’umma” inji shi.
KARANTA WANNAN LABARIN: An yi dauki ba Dadi tsakanin yan bindiga da soji a Abuja
” Martaba Sarki mutum ne guda, wanda ya tsaya cif-cif, tare da kame kansa. Ya kasance Mai haba-haba da maraba ga jama’a, Halinsa na kwarin gwiwa da lumana ya na bada gudumma wa ba kaɗan ba, wajen buɗe yankinsa da haɓaka sauyin tattalin arzikin yankin, hakika zai yi matukar wahala a iya cike gurbin shi” inji Sanata Uba Sani.
A Karshe Sanatan ya ce, “Ina mika Sakon ta’aziyata ga Iyalin Sarkin, HH Dr Barde, da daukacin jama’ar Karamar hukumar Chikun da Mai Girma, Gwamna Nasir El-Rufai da sauran jama’ar Jihar Kaduna, kan wannan rashin da ba zamu iya hanawa ba.” Kamar yarda Uba Sani ya bayyana.
“Muna fatan ran masoyi kuma Mahaifinmu mai Sarauta ya huta cikin cikakkiyar salama”