Hukumomin Najeriya da Nijar sun gana jiya litinin a birnin Maiduguri na jihar Borno domin magance musabbabin rikicin da ya addabi kasashen biyu.
Babban sakataren hukumar hadin gwiwa tsakanin Najeriya da Nijar, Ambasada Rabiu Akawu, ya ce an kira taron ne da nufin lalubo hanyoyin warware matsalolin tsaro da kasashen biyu ke fuskanta sama da shekaru goma.
Da ya ke jawabi a yayin taron kwamitin hadin gwiwa na bangarorin biyu (LBC) da ya shafi jihohin Borno da Yobe na Najeriya da yankin Diffa na Jamhuriyar Nijar ya ce;
“Saboda haka kwamitin ya yi kira da a dauki matakin hadin gwiwa, matakin kasa da kuma daidaita iyakokin kasa da Samar da mafita,” inji shi.
KARANTA WANNAN LABARIN: Jami’ar Lokoja Ta Dauki Mafarauta Domin Tabbatar da Tsaro a Jami’ar
Ya kuma bukaci mahalarta taron da su fito da shawarwari masu amfani da za su zakulo musabbabin tada kayar bayan, tare da kuma kididdige rawar da al’ummar yankin ke takawa wajen tabbatar da tsaro da tabbatar da doka da oda a yankunansu.
Taron, in ji shi, ya kuma tattauna batutuwan da suka shafi samar da abinci, kiwon lafiya, sufuri, wasanni da ayyukan da suka shafi matasa.
Anashi bangaren Sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, ya ce rashin aikin na LBC ya taimaka wajen karuwar rashin tsaro a jihohin da ke kan iyaka da kasashen biyu.
Da yake jawabi Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya ce akwai bukatar a magance matsalolin samar da ababen more rayuwa na al’ummomin da ke kan iyaka.