Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya yi jimamin rasuwar Olubadan na Ibadan, Oba Saliu Adetunji wanda aka sanar da rasuwarsa ranar Lahadi yana da shekaru 93 a duniya.
Gwamnan a cikin wata sanarwa da babban sakataren yada labaran sa, Muhammed Onogwu ya rabawa manema labarai yayin da yake mayar da martani game da rasuwar mahaifinsu, ya bayyana rasuwarsa a matsayin rashi na kasa ganin cewa Najeriya ta yi rashin wani babban uban gargajiya.
Gwamna Bello ya yi nuni da cewa, duk da cewa mutuwar tasa ta zo a lokacin da ya tsufa sosai, amma aikin da yake yi na neman zaman lafiya da hadin kai zai kasance cikin kewar sa a jihar da yankin da ma kasa baki daya.
Yayin da yake jajantawa majalisar gargajiya ta jihar Oyo da gwamnatin jihar Oyo da daukacin yankin kudu maso yamma bisa rasuwar sarkin, gwamna Bello ya bayyana cewa sarkin ya yi rayuwar da ya jagoranci al’ummarsa wanda hakan babban nasara ce.
Gwamnan ya kuma mika ta’aziyyarsa ga iyalan marigayi Olubadan, inda ya bukace su da su jajantawa ganin yadda mahaifinsu ya yi rayuwa mai kyau a duniya.
Gwamna Bello ya yi addu’ar Allah ya baiwa marigayi sarki hutu na har abada, sannan kuma ya baiwa yan uwa hakuri da karfin halin jure irin wannan rashi.