Tsohon mataimakin shugaban kasa, kuma dan takarar shugaban kasa a zaben 2019, Atiku Abubakar a sakon da ya aike na tunawa da ranar ‘yancin Nijeriya ya yi Allah-wadai da take hakkin bangaren shari’a da take hakkin fadar albarkacin baki da na ‘yan jarida da gwamnatin Buhari ke yiwa ‘yan kasa.
Atiku ya bayyana cewa lallai gwamnatin Buhari na take bangaren shari’a da abin da ya kira rashin ‘yancin bangaren kafafen watsa labarai.
Atiku ya bayyana hakan ne a cikin sanarwar da ya fitar a ranar Litinin, inda ya tabbatar da cewa wadanda suka yi fafutikar ‘yantar da Nijeriya ba su taba tunanin cikin shekara 59 da samun ‘yancin kai Nijeriya za ta fuskanci koma baya haka ba.
Atiku ya ce akwai bukatar a bar bangaren shari’a da na kafafen watsa labarai su ci gashin kan su, tare da barin matasa masu gwagwarmaya su yi fafutikarsu, domin a cewarsa matasan nan sune fatan Nijeriya.