Rahotanni da suka fito daga jamhuriyyar Nijer sun nuna cewa; Nijeriya da makwabciyarta ta jamhuriyyar Nijer sun gudanar da wani zama na musamman domin tattauna yadda za su gama da ‘yan bindiga a kasashen biyu wanda suka tagayyara mutanen kasar su sakamakon hare-haren su.
Kamarin Hare haren ‘yan bindiga kan iyakar Nijar da Nijeriya da ke kisa da satar mutane don neman kudin fansa, satar shanu da saka dubban iyalai gudun hijira ya sa gwamnonin Jihohin Katsina, Sokoto da Zamfara suka halarci taron kwanaki biyu da gwamnan Maradi Zakari Umaru ya shirya don daukar matakai a kan wannan matsala ta tsaro.