Shugaban hukumar kula da hana yaduwar cututtuka ta kasa wato NCDC, Chikwe Ihekweazu ya bayyana cewa Nijeriya za ta bukaci Naira Biliyan hudu domin hana bullowar cututtuka a kasar. Ihekweazu ya fadi haka a taron tsara hanyoyin hana bullowar cututtuka a Nijeriya wanda aka yi a jihar Legas. Ihekweazu ya ce sun shirya wannan taro ne domin hada kawance da kungiyoyin masu zaman kan su domin dakile yaduwar cututtuka a kasar nan.
Ya ce; a lokacin da cututtukan bakon dauro, sankarau, kwalara, ‘monkey pox’ da sauran su suka bullo hukumar ta NCDC ta taka muhimmiyyar rawa wajen ganin an dakile yaduwar cututtukan. Ihekweazu ya ce idan ana bukatar a sami sakamako na dindindin sai fa an ware Naira biliyan 4 domin haka. Ya kara da cewa; sai dai gwamnati ba za ta yi hakan ita kadai ba musamman yadda kungiyoyi masu zaman kansu ke da muhimmiyar rawa da za su iya takawa don samarwa mutanen kasar kiwon lafiya ta gari. Ya karkare a cewa; a yanzu dai hukumar na kokarin tsaro hanyoyin da za su fi dacewa domin ganin hakan ya faru musamman yadda babu wanda ke da masaniyar ranar da wata cutar za ta sake iya bullo.