Ministan Gona da ci gaban karkara, Sabo Nanono, ya bayyana cewa Nijeriya ta cimma kashi 80 wajen bunkasa ayyukan manoma a kasar. Sabo Nanono, ya bayyana hakan ne a wani taro da aka shirya dangane da ayyukan noman damina a Nijeriya wanda hukumar NAERLS ta shirya a ranar Alhamis a Abuja.
Nanono, ya bayyana gamsuwarsa bisa nasarar da ake samu a bangaren, inda ya ce; ba a gaza ba, kuma yana fatan zuwa shekara mai zuwa a kai inda ake so a je.
Sabo Nanono, ya ce hukumar NAERLS ita ta gano irin wannan nasarar da aka samu, inda ya jaddada cewa; akwai bukatar muhimmantar da tattara bayanai domin bunkasa bangaren noman a Nijeriya.