Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranar Juma’a 1 ga watan Oktoba a matsayin hutu don bukukuwan cikar kasar shekara 61 da samun ‘yancin kai.
Ministan harkokin cikin gida Rauf Aregbesola ne ya sanar da hakan a madadin gwamnatin tarayyar.
Ya taya ‘yan kasar murna yana mai cewa gwamnati ta mayar da hankali wajen kawo karshen dukkan kalubalen da kasar ke fuskanta.
“Kasa mai yawan al’umma kusan miliyan 200 kuma mutanen sun kasance masu basira da kwazo, kuma masu haskawa tamkar daiman. wato matsayin yawan shekarun da kasar ta kai.
“‘Yan Najeriya na sheki tamkar daiman a cikin kwali, daga wadanda suke bangaren ilimi zuwa kasuwanci da kirkire-kirkire da wake-wake da fina-finai da nishadi da ado da al’adu.
“Mu ne kasar Afirkan da ke kan gaba a duniya kuma abar alfahari nahiyar Afirka,” a cewar Aregbesola.
Nijeriya ta samun ‘yancin kai daga Turawan mulkin mallaka ne ranar 1 ga watan Oktoban 1960.
Ministan ya jaddada cewa murnar cikar shekara 61 da samun ‘yancin Nijeriya na da muhimmanci, amma lafiyar ‘yan kasar ce gaba da komai a wajen shugaban kasa, musamman ma a wannan lokaci da ake damuwa kan yadda cutar korona nau’in Delta ke ci gaba da bazuwa a kasar.
Don haka ya ce a bana ba za a yi wasu bukukuwa kamar yadda aka saba ba.