Daga Sulaiman Musa
Kasar Nijeriya ta aike da dakarunta na ‘yan sanda da yawansu ya kai 144 zuwa kasar Somaliya domin kokarin wanzarwa da tabbatar da zaman lafiya.
Jami’an wadanda suka tafi a karkashin shirin Tarayyar Afirka na samar da zaman lafiya a Somalia da a takaice ake kira (AMISOM).
Sanarwar da EU ta wallafa a shafinta na yanar gizo-gizo ta bayyana cewa ‘yan sandan za su kwashe shekara guda suna aikin wanzar da zaman lafiya a can Somalia, wanda ke fama da hare-haren mayakan kungiyar Al-Shabaab.
“A shekara dayan da za su yi za su bayar da shawarwari da kuma dabaru na aiki ga rundunar ‘yan sandan Somaila,” in ji sanarwar.
Ta kara da cewa, lokacin da suka isa Mogadishu a jirgin sama daga babban birnin tarayyar Nijeriya, Abuja, jami’an ma’aikatar lafiyar Somalia sun yi wa ƴan sandan na Nijeriya gwaje-gwajen lafiya kamar yadda ake yi domin koauce wa kamuwa da cutar korona inda daga bisani jami’an ‘yan sandan AMISOM suka yi musu jawabi.