Gwamnatin tarayya ta sanar da ranar dawo da jigilar jiragen sama na ƙasashen waje. Ministan Sufurin jiragen sama, Hadi Sirika ne ya wallafa bayanin haka a shafinsa na Twitter, inda ya ce za a fara jigilar ne zuwa ƙasashen waje daga ranar 29 ga watan Agustan 2020.
Sai dai Ministan ya ce, za a fara hakan ne da filin jirgin sama na Legas da Abuja kamar yadda aka fara da dawo da jigilar jirage a cikin Nijeriya.
Ya kuma tabbatar da cewa za a sanar da matakai da ka’idoji a nan gaba kaɗan.