Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa Nijeriya za ta duba yiwuwar sake bude ofishin Jakadancinta dake birnin Colombo a kasar Sri Lanka wacce ta rufe a 2017. Inda shugaban kasar ya ce bisa duba da alakar dake tsakanin kasashen biyu, ya sanya za a sake budewa.
Shugaban kasar ya bayyana hakan ne a yayin da yake bankwana da Jakadan kasar Sri Lanka din, Thambirajah Raveenthiran a fadar shugaban kasa dake Abuja a ranar Talata.
Shugaban kasar ya ce matsalar tattalin arziki da ofishin Jakadancin ya fuskanta ya sanya aka rufe shi a wancan lokacin. Sai dai shugaban kasar ya tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta dauki wadansu matakan da ya kamata wajen farfado da ofishin jakadancin.