NiMet ta yi Gargaɗi, tace za’a samu Mamakon Ruwan Sama na Kwanaki 4 a Abuja, da Jihohi 5
Hukumar Yanayi ta Najeriya (NiMet), a cikin hasashenta na baya-bayan nan, ta yi hasashen za a yi ruwan sama kamar da bakin kwarya na kwanaki hudu a jihohi biyar na arewacin kasar, da kuma babban Birnin Tarayya Abuja.
Jihohin da mamakon ruwan sama zai shafa sun hada da wasu sassan Kaduna, Niger, Bauchi, Plateau, Nasarawa, da kuma Babban Birnin Tarayya Abuja.
KARANTA WANNAN LABARIN: 2023: Ya kamata INEC ta haramtawa Ƴan Takarar da ke ziyartar coci-coci da masallatai – Adeyanju
NiMet a cikin rahotonta na yanayi na baya-bayan nan ya bayyana cewa ana kuma sa ran za a samu ruwan sama mai matsakaici a jihohi kamar Kwara, Oyo, Kogi, Ogun, Ekiti, Ondo, Sokoto, Katsina, Zamfara, Kebbi, Kano, Jigawa, Yobe, Borno, Gombe, Adamawa, Taraba, Benue, Cross River, Akwa Ibom, Ebonyi, Enugu, Abia, Imo, Anambra, Rivers, Edo da Delta.
Rahoton ya ce ana sa ran samun ruwan sama kadan a wasy sassan kasar nan a cikin wa’adin da aka yi nazari akai.
“Yayin da ake sa ran samun ruwan sama kadan ko babu a jihohi kadan. Sakamakon mamakon ruwan sama da ake sa ran za a yi a wasu sassan tsakiyar biranen kasar da kuma madaidaicin ruwan sama da ake sa ran za a samu a yankin kudu maso gabashin kasar na tsawon kwanaki biyu a jere, ana saran yiwuwar afkuwar ambaliyar ruwa a kan tituna, da kananan Matsugunni da Magudanan Ruwa.
“Har ila yau, ana sa ran ruwan sama mai matsakaici da mai yawa zai kasance, tare da iska mai karfi musamman a jihohin arewa da tsakiya a lokacin hasashen.
“Saboda haka, ana shawartar jama’a da su guji lungu da saƙo na kasa, kada su yi tuƙi cikin ruwa, su share magudanun ruwa, da guje wa tsayawa a karkashin bishiyoyi da wuraren da ba su da tsaro a lokacin damina, da kashe na’urorin lantarki kafin ruwan,”.
A wani labarin kuma: 2023: Ya kamata INEC ta haramtawa Ƴan Takarar da ke ziyartar coci-coci da masallatai – Adeyanju
Wani mai fada a ji a shafukan sada zumunta, Deji Adeyanju, ya buƙaci Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta haramtawa yan takarar da ke ziyartar coci-coci ko Masallatai domin neman goyon baya gabanin babban zaɓen 2023.
Jaridar DAILY POST ta rawaito cewa daga majami’u zuwa masallatai har ma da wuraren ibada, ana ganin wasu ƴan takara na tafiya daga wannan wuri zuwa wani wuri suna neman ƙuri’u.