Daga: Abbas Yakubu Yaura
Hukumar kula da yanayi ta Najeriya (NiMet) ta yi hasashen cewa za’a samu tsawa da ruwan sama daga ranar Laraba zuwa Juma’a a fadin kasar.
Hasashen Yanayi da NiMet ta fitar a ranar Talata a Abuja tace za a yi tsawa a sassan jihohin Katsina, Kano, Kaduna, Jigawa, Bauchi, Gombe, Kebbi, Zamfara, Sokoto da Taraba a safiyar ranar Laraba.
KARANTA WANNAN LABARIN: 2023: Jam’iyyar NNPP Ce Kadai Za Ta Iya Kwace Kujerar PDP A Akwa Ibom – Akpanudoedehe
A cewarta, ana sa ran za a yi tsawa a ware a wasu sassan Jigawa, Bauchi, Adamawa, Sokoto, Zamfara, Gombe, Taraba, Kano, Kaduna, Katsina, Borno da kuma Yobe.
” Ana sa ran za a yi ruwan sama a yankin Arewa ta tsakiya inda za a yi ruwan sama a sassan babban birnin tarayya, Filato da Neja da safe da yardar Allah.
“Da rana da yamma ana tsammanin samun ruwan sama a sassan babban birnin tarayya, Filato da Neja idan Allah ta amince.
“An yi hasashen samun ruwan sama a kan Ciki da Biranen Gabas na Kudu da safe.
“A cikin sa’o’i na rana da yamma, ana tsammanin sa ran samun saukar ruwan sama a sassan Enugu, Anambra, Ondo, Ekiti, Edo, Delta, Rivers, Bayelsa, Akwa Ibom, Lagos da Cross River,” in ji NiMet.
Hukumar ta kuma yi hasashen yanayin samun kadawar iska da kuma hadiri a yankin Arewa a ranar Alhamis inda ake sa ran za a yi tsawa a sassan Kebbi, Sokoto, Katsina da Zamfara.
NiMet ta yi hasashen zazzafar tsawa a sassan Borno, Kebbi, Kano, Adamawa, Kaduna, Taraba, Gombe, Sokoto da Bauchi da yammacin ranar idan Allah ya yarda.
“Ana sa ran da sanyin safiya a yankin Arewa ta tsakiya tare da yiwuwar samun ruwan sama a sassan babban birnin tarayya, Neja da kuma Benue idan mai duka ya amince.
“Da rana da yamma ana sa ran samun ruwan sama a sassan Kogi, Neja, Nasarawa, Benue, Filato da Babban Birnin Tarayya Abuja.
“An yi hasashen samun ruwan sama a kan Ciki da Biranen Gabas na Kudu da rana.
“Ana sa ran samun ruwan sama a sassan Edo, Delta, Osun, Ondo, Ebonyi, Imo, Ogun, Ondo, Edo, Abia, Bayelsa, Delta, Lagos, Cross River, Rivers da Akwa Ibom a lokacin rana da yamma.” Hukumar ta ce.
Hukumar ta yi hasashen yanayin samun kadawar iska da kuma hadiri a yankin Arewa a ranar Juma’a inda za a yi tsawa a sassan Borno da Adamawa da safe.
Ta yi hasashen samun tsawa a sassan Yobe, Borno, Bauchi, Gombe, Taraba da Jigawa da rana.
“An yi hasashen da safiye a yankin Arewa ta tsakiya da yiwuwar samun ruwan sama a sassan babban birnin tarayya, Neja da Filato.
“A washegari, ana sa ran samun ruwan sama a sassan babban birnin tarayya, Benue, Neja da Nasarawa.
“Ana hasashen samun ruwan sama a kan kasa da garuruwan Kudu da ke bakin gabar teku da safe.
“Akwai yiwuwar samun ruwan sama a sassan Edo, Ondo, Osun, Oyo, Ekiti da kuma bakin teku a lokacin rana da yamma,” in ji shi.
A cewar NiMet, akwai yiwuwar samun ruwan sama na tsaka-tsaki a yankin Arewa, da Arewa ta tsakiya na kasar wanda ka iya haifar da ambaliya, an shawarci ‘yan kasar mazauna yankin da su yi taka tsantsan.
NiMet ta kuma shawarci hukumomin kula da gaggawa da su kasance cikin faɗakarwa.
“Zazzabi yana kan ƙananan ƙofa, an shawarci masu rauni da su kasance cikin dumi.
“An shawarci ma’aikatan jiragen sama da su sami sabbin rahotannin yanayi daga NiMet don samun ingantaccen shiri a ayyukansu,” in ji hukumar. (NAN)