A wani mataki na bunkasa bangaren labarai, kimiyya da kyuma fasaha wato ICT a takaice, hukumar lura da ci gaban sadarwa ta kasa wato NITDA ta hada hannu da gwamnatin jihar Nasarawa domin ganin sun bunkasa wannan fannin.
Gwamnan jihar Nasarawa, Injiniya Abdullahi Sule ya kai ziyara a ranar Alhamis ofishin Babban Daraktan hukumar NITDA din, wato Kashifu Inuwa Abdullahi a babban hedikwatar hukumar dake Abuja.
A yayin da yake gabatar da jawabinsa, gwamnan ya jinjinawa hukumar bisa yadda suke gudanar da ayyukansu, inda ya bayyana bangaren ICT a matsayin jigo da yake tallafawa a bangaren kimiyya da fasaha. Gwamnan ya nemi hadin kan hukumar a bangaren ICT din ga al’ummar jihar Nasarawa, domin ganin an horas da su ilimin sashen domin ci gaban jihar.
Daraktan NITDA, Kashifu Inuwa Abdullahi CCIE da yake maida jawabi, ya nuna jindadinsa da aka samu gwamna kamar sa da yake da buri akan sashen ICT, da kuma yunkurin da yake son dauka na bunkasa bangaren ICT din domin ci gaban kasarnan. Kashifu ya ce a kofa a bude take a koyaushe, kuma hukumarsu a shirye take wajen hada hannu da gwamnan domin bunkasa bangaren ta hanyar samar da ayyukan yi, da haraji a kasarnan.