Hukumar gudanarwar Jami’ar Sule Lamido dake Kafin-Hausa a jihar Jigawa, a ranar Laraba ta bayyanawa cewa ta sami tallafin Kwamfuta 100 a karkashin cibiyar labarai da bayanai da fasaha daga hukumar ci gaban yada labarai ta kasa wato NITDA a turance
Jami’in huld da jama’a na Jami’ar, Alhaji Sadiq Lawal, shi ne ya bayyanawa manema labarai hakan a garin Kafin-Hausa, inda ya ce; Jami’in Kimiyya na NITDA din wato Kehinde Owopetu, shi ne ya mika Kwamfuta din kirar ‘Laptops’ a madadin NITDA din.
Ya tabbatar da cewa; mataimakin shugaban makarantar, Dr. Umar Maisaje shi ne ya karbi Kwamfuta din a madadin shugaban Jami’ar. Lawal ya ce Jami’ar ta yi farin ciki da wannan kyautar da aka ba su, kuma za su yi amfani da su a aikin da suka dace.