Jami’an rundunar ‘yan sandan Najeriya, da ma’aikatan tsaro na farin kaya, sun tsaurara matakan tsaro a harabar majalisar dokokin tarayya da ke Abuja.
Kara jami’an tsaron na zuwa ne sakamakon zanga-zangar da kungiyar kwadago ta Najeriya ta shirya tare da hadin gwiwar kungiyar malaman Jami’o’i.
A ranar Talata ne ma’aikata a jihohi daban-daban na tarayyar kasar nan suka fara zanga-zangar, inda suka gargadi gwamnatin tarayya da ta amince da bukatun kungiyar ASUU domin ganin kungiyar malaman jami’o’in ta sake bude jami’o’in Najeriya da aka rufe sama da watanni biyar.
DUBA WANNAN LABARIN: Ba don Buhari ba da kasar Liberia bata samu zaman lafiyar yanzu ba
Wadanda suka jagoranci zanga-zangar a Abuja ranar Laraba sun hada da shugaban NLC, Ayuba Wabba; Dan takarar shugaban kasa na AAC, Omoyele Sowore, tsohon dan majalisa, Sanata Shehu Sani, shugaban ASUU, Farfesa Emmanuel Osodeke, da tsohon shugaban ASUU, Farfesa Biodun Ogunyemi, da dai sauransu.
A halin yanzu dai suna jagorantar masu zanga-zangar zuwa majalisar dokokin kasar yayin da jami’an ‘yan sandan Najeriya da sauran jami’an tsaro ke jagorantar hanyar tabbatar da isassun tsaron rayuka da dukiyoyi.
Wani jami’in rundunar ‘yan sandan Najeriya da ya zanta da wakilinmu da ya nemi a sakaya sunansa, ya ce an tura su ne domin kare masu zanga-zangar, musamman duba da barazanar tsaro da ake fama da ita a birnin na Abuja.
A halin da ake ciki, shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, ya sanar da cewa majalisar ta shiga wani zama na sirri ne ‘yan mintoci kadan bayan masu zanga-zangar sun mamaye harabar majalisar a ranar Laraba.