Kungiyar Kwadago ta Najeriya reshen jihar Gombe, ta kara jan hankalin mambobinta da kungiyoyin farar hula, domin shiga zanga-zangar adawa da matakin gwamnatin tarayya na cire tallafin man fetur.
Shugaban kungiyar reshen jihar Gombe, Adamu Musa ne ya shaida wa manema labarai hakan, a wani taron tattaunawa da aka yi ranar Juma’a a gidan ma’aikata cewa cire tallafin man fetur zai kara jefa ‘yan Najeriya cikin wahala. Ya kuma ba da tabbacin cewa kungiyar NLC za ta yi duk abin da ya dace don ganin gwamnatin tarayya ta janye matakin na ta.
Kungiyar ta NLC ta tsayar da ranar 27 ga watan Janairu domin gudanar da zanga-zangar ta a fadin jihohi 36 da kuma babbar zanga-zangar da za a yi a Abuja kan shirin cire tallafin man fetur.
Adamu ya kara da cewa, “NLC na fatan bin umarnin ma’aikata da ‘yan kungiyar CSOs don bayar da hadin kai ga shugabanninsu da kuma fitowa domin shiga cikin lumana ba tare da cutar da kowa ba.”
Da aka tambaye shi game da shirin tabbatar da gudanar da zanga-zangar ba tare da wata tangarda ba, Adamu ya ce kungiyar ta tuntubi hukumomin tsaro domin tabbatar da gudanar da zanga-zangar lumana.