NLC zata shirya zanga-zangar kwana ɗaya kan Yajin Aikin ASUU, da wasu Ƙungiyoyi
Ƙungiyar Ƙwadago ta Ƙasa a ranar Alhamis tace zata gudanar da zanga-zangar kwana ɗaya, domin tilastawa Gwamnatin Tarayya ta biya dukkanin buƙatun Ƙungiyoyin Jami’o’i.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ɗaruruwan Ɗalibai sun tsallake rijiya da baya, bayan Gobara ta tashi a Makarantar Enugu
Ƙungiyar tace rahoto daga Kwamitin Ayyuka yaga akwai rashin samun cigaba da tattaunawar data kamata daga Shuwagabancin Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Kasa, da Ƙungiyar Manyan Ma’aikatan Jami’o’i, da Ƙungiyar Ma’aikatan Jami’o’i, da Ƙungiyar NAAT.
Shugaban Ƙungiyar Ayuba Wabba wanda yayi jawabi a lokacin bude taron Kungiyar na Kasa.
Wabba ya umarci dukkanin Ƙungiyoyi dake ƙarƙashin ta dasu fitar da sanarwar shirin zanga-zanga na kwana ɗaya daga sati mai zuwa.
“Inaga akwai rashin maida hankali akan magance matsalar yajin aiki, a saboda haka, Kwamitin Ayyuka na Ƙungiyar zata shirya zanga-zanga na kwana ɗaya, domin yin kira ga Gwamnati ta magance yajin aiki da sauri.
Amma bai bayyana ranar da zanga-zangar zata wakana ba.
Wabba ya bayyana rashin jindaɗi na ƙarancin man fetur a ƙasa, yana mai ƙara dacewa Ƙungiyar nayin karatu akan korar Malamai daga Gwamnatin Jahar Kaduna tayi.