Wani babban Pasto mai suna Adewale Giwa, ya karfafama Yarbawa da Inyamurai da su cigaba da fafutukar neman Yancin kai, don sun kusa samu nan da dan lokacin kadan. Kamar yadda Jaridar daily post ta wallafa a shafinta
Yace duba da abubuwan dake faruwa a kasar nan, inda jagororin masu fafutukar neman Yancin kai na Kasar Yarbawa Sunday Igboho da na yankin Inyamurai Nnamdi Kanu aka garkame su, na nuna cewa nasara na gaf da zuwa.
Yace babu wanda ya isa ya hana samun yancin kai daga mulkin fulani, suna cigaba da cutar da masu fafutukar neman yancin haka kuma nasarar su na kara kusantowa, Paston ya bayyana hakane a Jaridar daily post ranar Laraba.
KARANTA:- Yarana 10 da ƙanwata sun mutu sakamakon cin abinci mai guba – Magidanci ya bada labari
Cutar da mutane da razanar dasu kan neman yanci ba abunda zai kara musu sai karfin guiwa, nan da dan lokaci kadan Yan Najeriya za su samu nasara, kuma da akwai haske daga karshe.
Yarbawa da Inyamurai da sauran masu fafutukar neman yanci, su tsaya tsayin daka, Ubangiji zai kawo dauki, zai rusa azzalumai, Yan Najeriya basu taba tsammanin shugaban Kasa Muhammadu Buhari zai ci amanar su ba, da suka zabeshi a zaben 2015.
Kodayake an sami matsala tun farko, kuma mun koyi darasi daga haka, babu yadda yan kadan suyi fada da masu yawa, amma nasara na gaf da zuwa. Kamar yadda ya ayyana.
Idan baku manta ba Jagoran masu fafutukar kafa kasar Oduduwa watau Sunday Igboho an cafke shi a Jamhoriyar Cotonou Yana kokarin tsallake Kasar zuwa Jamus.
Sannan Nnamdi Kanu na tsare a ofishin Jami’an DSS sama da sati biyu kenan yanzu, bayan da Jami’an Najeriya suka cafke shi a kasar Kenya.
Comments 1