Shugaban Kungiyar Yan bindiga ta Kungiyar Inyamuran IPOB Nnamdi Kanu ya caccaaki yan wasan Super Eagles biyu Wilfred Ndidi da Kuma Kelechi Iheanacho bisa rike tutar Najeriya da suka yi bayan lashe kofin FA a ranar Asabar.
Dukkannin yan wasan biyu Iheanacho da Ndidi suna take wasa ne wa Ƙungiyar Leicester City ta kasar Birtaniya wacce kuma ita ta lashe kofin wanda ya zamo mata karon farko a tarihi.
Yan wasan wadanda Inyamurai ne su ma, sun ɗaga tutar ta Najeriya ne cikin farin ciki da nuna jin daɗi suna fara’a.
Wannan ne ya sa shugaban IPOB ɗin Nnamdi Kanu ya fatattake su tare da cewa sun ji kunya tun ba sa goyon bayan fafutuka da yake yi.
Cikin wani sako da ya wallafa a shafin Tuwita, Kanu ya kafa misali da dan wasan Barcelona dan asalin kasar Spaniya Gerard Pique inda ya ce ba ya boye goyon bayansa wa yankin Kataloniya da ita ma take shirin ɓallewa.