Tsohon Babban Mai Taimakawa Shugaban Ƙasa Goodluck Jonathan akan Harkokin Al’umma Dr Doyin Okupe, yayi kira ga Gwamnatin Tarayya data saki jagoran Ƙungiyar Tsagerun IPOB Nnamdi Kanu, idan har hakan zai samar da zaman lafiya a shiyyar Kudu maso Gabas.
Ya koka na yiwuwar samun faɗa a Jahar Anambra, yana mai nuni dacewar damar samun gudanar da rayuwa, da kuma rayuwar shugaban IPOB tafi zaɓen Gwamnan Anambra na 6 ga watan Nuwamba a Jahar, wanda yace akwai yiwuwar sojantar da aikin zaɓen.

KARANTA WANNAN LABARIN: Kotu ta tasa ƙeyar wani Matashin yayi lalata da yara 4 gidan yari a Rivers
Tsohon Mataimakin shugaban Ƙasar ya bayyana haka a cikin wata tattaunawa da majiyar jaridar Dimokuraɗiyya a Abuja akan zaɓen shuwagabannin Jami’iyyar PDP da akayi na ƙasa.
A cewar Okupe, Gwamnatin Jonathan data yanzu sun kashe biliyoyin Nairori, wajen yaƙi da Boko Haram amma har yanzu ba’a samu nasara ba.
Yace “zaɓen Jahar Anambra babu kokwanto shine abun kokwanton ƴan Najeriya
Comments 1