Kamfanin mai na kasa NNPC ya sanar da cewa ya lura da fara samun dogayen layuka a gidajen mai dake wasu sassan birnin tarayya Abuja.
A cewar kamfanin hakan dama ba abun mamaki bane musamman lokacin dogon hutu, baya ga bukukuwan sallah da ake ci gaba da gudanarwa a yanzu haka.
Guda cikin jami’an Kamfanin Garba Deen Muhammad, a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a daren jiya ya ce mazauna birnin tarayyar sukan dawo zuwa Abuja bayan kammala hutu a garuruwan su, wanda hakan shima yak an taimaka wajen karuwar dogayen layukan a gidajen man.
Garba Deen ya kara da cewa Kamfanin NNPC da Hukumar Kula da Man Fetur ta Najeriya tare da hadin gwiwar abokan huldarsu sun dauki matakan da suka dace don ganin ba a samu tsaiko ba wajen tasarrufi da man, ciki kuwa har da lita biliyan 2.5 ta man fetur din.
Kamfanin NNPC ya kuma tabbatarwa da mazauna birnin tarayyar dama yan kasa cewa yanzu haka kamfanin yana da mai isasshe da zai iya biyan bukatun yan kasarnan.
A karshe ya bukaci masu siya domin ajiye shi da su gujewa hakan, kuma nan da wasu kwanaki yawan man zai karu.