NNPP ta samu Sabbin Shuwagabanni a Nasarawa, tasha alwashin ƙwace Kujerar Gwamna Sule a 2023
Jam’iyyar Mai Alamar Kayan Marmari NNPP ta ƙaddamar da sabbin shugabannin ta a Jahar Nasarawa, wanda zasu jagoran ci harkokin Jam’iyyar zuwa Shekaru huɗu.
Jam’iyyar, a lokacin da take ƙaddamar da shugabannin ta da suka samu nasara ta hanyar sasanci daga faɗin Ƙananan Hukumomi 13 na Jahar a lokacin zaɓen ta, tasha alwashin ƙwace Kujerar Gwamnan Jahar Nasarawa a Shekarar 2023.
Dayake jawabi a Lafia a ranar Talata, Sabon Shugaban Jam’iyyar Sidi Bako yace Jam’iyyar NNPP tana buƙatar shugabanci mai kyau domin ta kawo romon Dimokuraɗiyya ga Mazauna Jahar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Komi Yayi Zafi: Lauya ya Maka Ƙungiyar su Ta Lauyoyi a Kotu, ya nemi a biyashi Miliyan 10
Yace “Jam’iyyar NNPP nada shugabanni masu ƙarfi a faɗin Ƙananan Hukumomi 13 na Jahar, kuma ina farin cikin sanar daku cewa Jam’iyyar mu zata samu nasara a Babban Zaɓen Shekarar 2023, domin mazauna garin su kurɓi romon Dimokuraɗiyya
” Bama goyon bayan Siyasar Uban gida da kuma ƙaƙaba Ɗan takara, wanda Al’umma basa so. Wannan jam’iyya zata baiwa mutane dama su zaɓi Shuwagabannin su da kan su.
“Jam’iyyar nada Mataimakan Shugaban Jam’iyya guda uku a faɗin shiyyoyi uku, da kuma sauran jami’ai Da suke a shirye domin cigaban Jam’iyyar. Da yardar Allah, zamu karbi ragamar Shugabanci a Shekarar 2023.”
Tunda Farko, Sakataren Jam’iyyar na yankin Arewa ta Tsakiya Umar Auta yace Jam’iyyar nada manufar samar da kyakkyawan Shugabanci a Jahar dama Ƙasa baki ɗaya.
Rahotanni sun nuna wasu daga cikin waɗanda aka zaɓa akwai Thomas Luka, Sakatare Ladan Ɗanlami, Ma’aji Nasir Mariga, odita-Janar, da sauran su.