Hukumar horaswa ta Nijeriya wato NOA a ranar Talata a lokacin bukuwan tunawa da ranar ‘yancin kai, sun yi kira ga ‘yan Nijeriya da su zama masu kishin kai tare da goyon bayan tsare-tsaren gwamnati.
Zubair Galadima wanda shi ne Daraktan NOA din reshen karamar hukumar Soba dake jihar Kaduna, shi ne ya bayyana hakan a Kaduna. Zubair Galadima ya ce Nijeriya na kan turbar ci gaba tun bayan samun ‘yancin kanta a shekarar 1960.
Ya tabbatar da cewa; Nijeriya ta samu ci gaba a bangarori daban-daban da suka hada da tattalin arziki, da kuma zamntakewa da wadansu sashe da ya hada ilimi. Inda ya ce yanzu haka ana da manyan makarantun gaba da Sakandare da suke karantar da ilmummuka daban-daban.